in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da dandalin tattaunawa kan samar da kayayyaki da zuba jari a tsakanin Sin da Nijeriya a yankin ciniki cikin 'yanci na Lekki
2017-03-25 13:23:14 cri

 

Ofishin jakadancin kasar Sin dake Nijeriya, da ma'aikatar kula da ciniki da masana'antu da zuba jari ta kasar, sun gudanar da wata tattaunawa kan hanyoyin zubar jari tsakanin Sin da Nijeriya, a yankin ciniki cikin 'yanci na Lekki dake jihar Lagos na kasar.

Yayin taron da ya gudana jiya Jumma'a, Jakadan Sin a Nijeriya Zhou Pingjian ya bayyana cewa, dandalin tattaunawar wani bangare ne na jerin tattaunawa kan tsarin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Nijeriya da aka amince da gudanar da shi bayan shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya ziyarci kasar Sin.

Wannan dai shaida ce da ke nuna manufofin kasar Sin a Afirka da suka hada da sada zumunta da hadin gwiwa tare da warware matsaloli tare da kasashen nahiyar cikin gaskiya.

A cewarsa, Sin da Nijeriya su ne manyan kasashe masu tasowa wadanda suka kulla dangantaka da juna ta hanyar hadin gwiwa a muhimman bangori.

Wa'adin aiwatar da shirin farfado da tattalin arziki na Nijeriya wato ERGP ya kusa yin daidai da wa'adin aiwatar da shirin shekaru 5 na raya kasar Sin karo na 13. Inda ake aiwatar da dukkan shirye-shiryen biyu domin kyautata tsarin tattalin arzikin kasashen biyu.

A nasa bangare, babban direktan hukumar lura da harkokin kirar motoci na Nijeriya Engr. Aminu Jalal ya bayyana cewa, gwamnatin Nijeriya ta ba batun bunkasa masana'antu muhimmanci duba da rawar da za su iya takawa wajen samar da tattalin arziki mai dorewa.

Engr. Aminu Jalal ya kara da cewa, yana fatan gwamnatocin kasashen biyu za su yi amfani da dandalin tattaunawar wajen fadada hadin gwiwarsu a yankin Lekki, ta yadda za su mori juna. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China