Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya ce, tanade-tanaden da ke cikin rahoton kasashen duniya game da kare hakkin dan Adam na shekarar 2016, wanda ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta kaddamar a kwanan baya, ba su da kan gado, kuma Amurka tana kallon kasar Sin da tunaninta. Kasar Sin ta ki amincewa da rahoton, har ma ta tuntubi Amurkar a hukumance.
A yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing, Geng Shuang ya ce, har kullum kasar Sin na tsayawa kan yin tattaunawa da mu'amala a tsakanin kasa da kasa a harkokin da suka shafi kare hakkin dan Adam bisa ka'idar yin zaman daidai wa daida da girmama juna, a kokarin yin koyi da juna da samun ci gaba tare.
Geng Shuang ya ce, kasar Sin ta kalubalanci Amurka da ta rika kallon kasar Sin a fannin harkokin da suka shafi kare hakkin dan Adam bisa yadda abubuwa suka kasance a zahiri kuma cikin adalci, sannan ta daina fakewa da sunan kare hakkin dan Adam tana tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin. (Tasallah Yuan)