in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da sakataren harkokin wajen kasar Amurka
2017-03-20 13:18:12 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da sakataren harkokin wajen kasar Amurka Rex Tillerson a jiya Lahadi a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, inda yayin ganawar shugaba Xi ya ce,

"Maraba da zuwanka kasar Sin Malam Tillerson, ina mai matukar farin cikin ganawa da kai. A wani sabon babi da muka shiga na kokarin raya huldar dake tsakanin Sin da Amurka, ka yi kokari sosai wajen yaukaka dankon zumuncin dake tsakaninmu. "

Yayin ganawarsu, shugaba Xi Jinping ya ce huldar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka na fuskantar wata muhimmiyar dama. Kuma Kamata ya yi a yi kokarin karfafa aminci a tsakanin bangarorin 2, ta yadda za su kara fahimtar juna.

A cewar shugaban kasar Sin, ya kamata a yi hangen nesa wajen kula da dangatakar dake tsakanin kasashen 2, da habaka hadin gwiwarsu, don tabbatar da moriyar juna. Sa'an nan, bangarorin 2 su kara yin musayar ra'ayoyi dangane da wasu manyan batutuwan dake jan hankalin duniya.

Ya kara da cewa, kamata ya yi a girmama moriyar da kasashen za su samu a dukkan bangarori, da daidaita batun da ake mai da hankali a kai, ta yadda za a samu damar tabbatar da kwanciyar hankali bisa dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka. Yana mai cewa, daga bisani kuma, sai a karfafa wa jama'ar kasashen 2 gwiwa, domin su kara yin mu'amala da juna, da nufin inganta dangantakar kasashen daga tushe. A cewar shugaba Xi,

"Na riga na tattauna da shugaba Donald Trump ta wayar tarho har karo 2, tare da rubuta masa sakonni 3. Dukkanmu na ganin cewa, ya kamata a samu karin hadin gwiwa tsakanin kasashenmu 2, tare da fatan ganin an shiga wani sabon babi na kyautata huldar dake tsakaninmu."

Shugaban kasar Sin ya ce yana fata jami'an gwamnatocin kasashen 2 za su kara yin musayar ra'ayi, don habaka hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin 2 a fannoni daban-daban. Sa'an nan a yi kokarin daidaita wasu batutuwan da suke jan hankalin kasashen, tare da ciyar da huldar dake tsakaninsu gaba.

A nasa bangaren, Mista Tillerson ya mika gaisuwa ga shugaba Xi Jinping, a madadin Donald Trump, shugaban kasar Amurka. Inda ya ce, shugaba Trump ya ba tattaunawar da ya yi da shugaba Xi Jinping na kasar Sin , ta wayar tarho muhimmanci sosai. A cewar Mista Tillerson,

"Shugaba Trump ya dauki tattaunawar da ya yi da shugaba Xi Jinping a matsayin wani batu mai muhimmancin gaske. A ganinsa, tattaunawar ta ingiza mu'amala tsakanin shugabannin 2, da sanya shi kara fihimtar kasar Sin da muhimmancin huldar dake tsakaninsu. Ban da haka kuma, shugaba Trump na dakon samun damar kai ziyara a kasar Sin, ta yadda za a samu karin fahimtar juna, da karfafa alakar dake tsakanin kasashen 2, tare da samar da wani yanayi mai kyau ga hadin gwiwar da za a yi tsakaninsu a nan gaba."

A cewar Rex Tillerson, sakataren harkokin wajen Amurka, kasarsa na son raya huldar dake tsakaninta da kasar Sin bisa wasu manyan manufofi, wadanda suka hada da magance rikici, da girmama juna, da hadin kai don moriyar juna.

Har ila yau, shugaba Xi Jinping ya nemi Mista Tillerson ya isar da sakon gaisuwarsa ga takwaransa na Amurka Donald Trump, sannan ya shaida masa cewa, yana maraba da zuwansa kasar Sin domin ziyarar aiki.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China