in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a yi takara da hadin gwiwa yayin da ake raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka
2017-01-25 13:43:06 cri

Sakamakon rantsuwar kama aikin da sabon shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi, ana hasashen fuskantar yanayi na rashin tabbas a duniya. Don haka ne ma dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka ke kara jawo hankalin duniya matuka.

Shugaban sashen nazarin harkokin Amurka na kwalejin nazarin batutuwan duniya na kasar Sin Teng Jianqun, na da ra'ayin cewa, za a shiga wani lokaci na daidaitawa da juna, yayin da ake raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Kana za a kara fadada takara da juna, da kuma hada kai a nan gaba.

Da yammacin jiya Talata 24 ga watan nan ne kungiyar 'yan jarida ta kasar Sin, ta gudanar da wani taron tattaunawa kan makomar dangantaka tsakanin Sin da Amurka, bayan da shugaba Donald Trump ya kama aiki a matsayin sabon shugaban kasar Amurka.

A gun taron, Shugaban sashen nazarin harkokin Amurka na kwalejin nazarin batutuwan duniya na kasar Sin Teng Jianqun, ya bayyana cewa yanzu kasar Amurka ba ta kai ga kawar da mugun tasirin da rikicin hada-hadar kudi na duniya na shekarar 2008 ya kawo mata ba, kana jama'a na nuna rashin jin dadi ga yanayin siyasar kasar Amurka, a lokacin da Trump ya hau kujerar shugaban kasar. A halin yanzu, kasar Sin tana kokarin shiga harkokin kasa da kasa da na yankuna. Bisa tushen fuskantar sauye-sauye a yanayin kasashen biyu, da matsayinsu a duniya, za a shiga lokacin daidaitawa da juna har na tsawon shekara daya, ko daya da rabi mai zuwa, domin raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka. Mr Teng ya bayyana cewa,

"A ganina, za a samu sabon canji yayin da ake raya dangantaka tsakanin Sin da Amurka. Game da irin wannan canji, na yi hasashe cewa, za a shiga lokacin daidaitawa da juna har na tsawon shekara daya zuwa daya da rabi a fannin raya dangantakar sassan biyu. Kasancewar Trump zai yi amfani da hanyar siyasa ta musamman wajen daidaita dangantakar dake tsakanin kasa da kasa, a nata bangare ma, Sin za ta gyara manufofin ta domin daidaita batun."

A ganin Teng Jianqun, kasar Sin za ta kasance muhimmiyar kasa da gwamnatin Trump za ta yi takara da ita. Bayan da aka gama yakin cacar baki, kasar Amurka ta rika sauya kulawar ta ga kasar Sin. Ya ce wannan ba bukatun Trump ba ne, bukatun zamantakewar al'ummar kasar Amurka ne. Har wa yau a nan gaba, Sin da Amurka za su fuskanci yanayin takara tare da na hadin gwiwa a lokaci guda, kuma bunkasuwar hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakaninsu, ba za ta taka muhimmiyar rawa kamar a baya ba, domin takara za ta karu tsakanin sassan biyu. Mr Teng ya ce,

"Bayan yakin cacar baka, musamman bayan shekarar 2000, kasar Amurka ta fara maida hankali ga kasar Sin. Trump zai ci gaba da bin wannan manufa. Don haka, Sin za ta kasance muhimmiyar kasa da gwamnatin Trump ta yi takara da ita, kana za su yi takara a fannonin tsaron kasa, da tattalin arziki da cinikayya. Ina tsammanin cewa, za a kara yin takara da hadin gwiwa da juna a tsakanin Sin da Amurka."

A karshen taron dai, Mr Teng ya yi nuni da cewa, kasashen Sin da Amurka za su cimma sabon tsarin yin mu'amala da juna, kuma yin mu'amala zai fi hadin gwiwa a tsakanin bangarori daban daban. Ana da kyakkyawar makoma kan dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka, koda yake za a samu rikici, amma ba zai yi tasiri ga hadin gwiwa da mu'amalar dake tsakaninsu ba. Duba da cewa Sin da Amurka suna dogaro da juna. Mr Teng ya bayyana cewa,  

"A gani na, Sin da Amurka za su kafa wasu sabbin tsare tsare. Domin a lokacin gwamnatin Barack Obama, an kafa wasu tsarin sarrafa matsalolin dake kasancewa a tsakaninsu, kamar shawarwari bisa manyan tsare-tsare, wadanda suka taka muhimmiyar rawa, wajen raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka. A takaice, ina da imani game da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, domin babu sauran wasu kasashe 2 kamar su a fannin dogara da juna a bangarorin siyasa, da tattalin arziki, da tsaron kasa. Koda yake suna da bambancin ra'ayoyi a wasu fannoni, amma za su ci gaba da raya dangantakarsu ta hanyar yin takara, tare da aiwatar da hadin gwiwa." (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China