in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dangantakar Sin da Amurka za ta shiga shekaru 36 a bana
2015-09-10 14:51:54 cri

Shekarar bana, shekara ce ta cika shekaru 36 da kulla dangantakar diflomasiyya tsakanin kasar Sin da kasar Amurka, cikin shekaru 36 da suka gabata, duk da cewa, kasashen biyu sun fuskanci wasu sabani a tsakaninsu, amma dangantakar kasashen biyu ta inganta bisa ka'idojin mu'amala da hadin gwiwa. A wani bangare, kasashen biyu sun habaka hadin gwiwa a fannoni daban daban, a dayan bangare kuma, kasashen biyu sun fuskanci sabani da bambancin ra'ayoyi a tsakaninsu. A yammacin ranar 9 ga wannan wata ne, ma'aikatar diflomasiyya ta kasar Sin ta shirya wani taron kara wa juna sani kan dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka, inda masana guda biyar da suka halarci taron suka tattauna yanayin dangantakar diflomasiyyar dake tsakanin Sin da Amurka a halin yanzu, da kuma kalubalolin dake gaban kasashen biyu a nan gaba.

Ga kuma rahoton da abokin aikinmu Ibrahim Yaya ya hada mana:

A yayin taron, wasu masana sun bayyana cewa, a matsayinsu na manyan kasashen biyu masu karfin tattalin arziki, yadda kasashen biyu ke raya dangantakar dake tsakaninsu na ci gaba da janyo hankulan kasa da kasa, a halin yanzu kuma, ba ma dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ke shafar kasashen kawai ba, har ma tana da muhimmiyar ma'ana ga kasashen duniya. Dangane da lamarin, mataimakin shugaban cibiyar nazarin harkokin kasa da kasa ta kasar Sin Ruan Zongze ya ce,

"Dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka ba kawai tana shafar batutuwan dake tsakanin kasashen biyu ko shiyya-shiyya ba, har ma tana shafar batutuwan dake tsakanin bangarori daban daban da sauran kasashen duniya."

Ban da haka kuma, wasu masana na ganin cewa, dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasar Amurka, muhimmin al'amari ne cikin harkokin siyasar duniya. Kwanan baya, an fidda wasu sabbin bayanai dangane da dangantakar kasashen biyu, inda ake ganin cewa, zai yi matukar wahala a samu wani ci gaba dangane da dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka. Dangane da lamarin, mataimakin shugaban kungiyar ma'aikatan diflomasiyyar kasar Sin Ma Zhengang ya ce,

"Wasu na ganin cewa, babu shakka wata rana za a yi yaki a tsakanin kasar Sin da kasar Amurka, ko da yake masu wannan ra'ayi ba su da yawa. Kana a 'yan shekarun nan, wasu masana ciki har da wasu shahararrun masanan Amurka sun fara bayyana cewa, dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasar Amurka ta shiga wani hali na gaba kura."

A watan Yunin wannan shekara, wani masanin kasar Amurka ya bayyana irin wannan ra'ayi, yana mai cewa, an samu babban canji a dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasar Amurka. A kullum kasar Amurka tana daukar kasar Sin a matsayin abokiyar gabarta, wannan ya sa, take daukar matakai masu gauni wajen matsa wa kasar Sin lamba.

Ra'ayin wannan masani ya janyo hankulan kasa da kasa, ko da yake masanan da suka halarci taron na jiya , sun musanta wannan ra'ayi.

Mataimakin shugaban kwalejin nazarin dangantakar kasa da kasa na jami'ar Renmin ta kasar Sin Jin Canrong ya bayyana cewa,

"Dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasar Amurka cike take da nuna gasa da kuma hadin gwiwa, ko da a shekarar bana, gasar dake tsakanin kasashen biyu ta dara batun hadin gwiwa, amma, babban tushen raya dangantakar kasashen biyu bai canja ba, haka kuma, gwamnatocin kasashen biyu na sauke nauyoyinsu yadda ya kamata, suna kuma ci gaba da tattauna yadda za a iya raya dangantakar dake tsakaninsu."

Haka kuma, shugaban sashen kula da harkokin kasar Amurka na cibiyar nazarin dangantakar kasa da kasa ta kasar Sin Da Wei ya bayyana cewa, a halin yanzu, kasashen duniya suna neman ci gaba ta hanyar yin hadin gwiwa. Bunkasuwar kasar Sin na bukatar kasar Amurka, ita ma, kasar Amurka na bukatar taimakon kasar Sin. Kasar Sin da kasar Amurka suna da moriyar iri daya kan batun da ya shafi tattalin arziki. Haka kuma, yana ganin cewa, dangantakar kasashen biyu na da cikin kyakkyawan yanayi. Ya ce,

"Akwai mu'amalar jama'a da al'adu yadda ya kamata a tsakanin kasar Sin da kasar Amurka. Yanzu haka akwai daliban kasar Sin kimanin dubu 270 dake karatu a kasar Amurka, yayin da akwai daliban kasar Amurka sama da dubu 20 suke karatu a kasar Sin. Sannan a ko wace rana, Sinawa da Amurkawa fiye da dubu 10 na yin tafiye-tafiye tsakanin kasashen biyu, lamarin da ya sa, mu'amalar dake tsakanin jama'ar kasashen biyu take da makoma mai haske."

Haka kuma, yana ganin cewa, mu'amalar al'adun jama'a dake tsakanin kasashen biyu za ta iya kawar da sabani da kuma rikicin dake tsakaninsu.

Shekarar bana, shekara ce ta kulla dangantakar diflomasiyya dake tsakanin Sin da Amurka, mataimakin shugaban cibiyar nazarin harkokin kasa da kasa ta kasar Sin Ruan Zongze ya ce, dangantakar kasashen biyu za ta ci gaba da bunkasa yadda ya kamta. Ya kara da cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai ziyarar aiki a kasar Amurka a wannan rana, lamarin da ya nuna cewa, za a shiga lokacin kaka na dangantakar kasashen biyu. Babu shakka ziyararsa za ta taimaka matuka wajen raya dangantakar kasashen biyu, kana, ya kamata kasashen biyu su hada kai da kuma daukar nauyinsu yadda ya kamata wajen raya dangantakar dake tsakaninsu, domin habaka sabbin hanyoyi wajen kafa wani sabon tsarin cimma moriyar juna tsakanin manyan kasashen biyu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China