Jamus ta dauki niyyar gaggauta korar bakin da suka aikaita laifuffuka
Gwamnatin kasar Jamus ta dauki niyya a ranar Talata na gaggauta korar bakin da suka aikata laifuffuka bayan hare haren ranar shiga sabuwar shekara kan mata a birnin Cologne da ake zargin wasu maza 'yan kasashen Larabawa da arewacin Afirka. Ministan cikin gidan Jamus, Thomas De Maiziere, da ministan shari'a, Heiko Maas, sun bayyana wannan mataki a yayin wani taron manema labarai, bayan tattaunawa a cikin kawacen shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel kan wasu shawarwari dake da nasaba da hare haren na Cologne. A cewar wadannan shawarwari, wadanda suka aikata laifuffukan, har ma yara da matasa, dole a tafi da su idan aka yanke musu hukunci mai tsanani kan manyan laifuffukan da suka aikata, hukuncin ya kasance ko a'a da sakin talala. Baki da masu neman mafaka su ma za su fuskanci hukunci mai tsanani a nan gaba idan aka tabbatar sun aikata fyade, sace-sace ko kin bada hadin kai tare da jami'an tsaro. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku