in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD ta koka da sabbin dokokin Amurka
2017-03-08 11:39:47 cri

Shugaban hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD Filippo Grandi, ya bayyana damuwa kan sabbin dokokin Amurka da ake kira da umarnin da shugaba Donald Trump ya rattabawa hannu a ranar Litini, yana mai jadadda bukatar kula da mutanen da suka gujewa rikici a kasashensu.

Mataimakin kakakin MDD Farhan Haq, yayin taron manema labarai na kulla yaumin, ya ruwaito Grandi na cewa, biyo bayan umarnin da Shugaban Amurka ya rattabawa hannu kan tsugunar da 'yan gudun hijira, Hukumar ta MDD ta jadadda cewa, 'yan gudun hijira mutane ne kamar kowa da rikice-rikice da tashen-tashen hankali suka tilasta musu tserewa daga kasashensu, da kuma ke bukatar daukin gaggawa.

Da yake tsokaci kan umarnin na Amurka, Grandi ya ce abu mafi muhimmanci shi ne, samar da kariya ga mutanen da suka tserewa rikici, inda ya ce sun damu da matakin, duk da cewa na wucin gadi ne, domin ya na iya kara jefa wadanda abun ya shafa cikin damuwa.

Farhan Haq ya ce Hukumar mai kula da 'yan gudun hijira za ta gana da Gwamnati Amurka don tabbatar da dukkan shirye-shiryen kula da 'yan gudun hijira sun kai matakin da ake so na kulawa da kariya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China