in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani rahoto ya bayyana cewa, daya bisa hudu na al'ummar Amurka na dauke da cutar amosanin gabbai
2017-03-08 11:06:52 cri

Cibiyar yaki da kula da cututtuka ta Amurka CDC, ta ce kusan daya bisa hudun balagai, kwatankwacin miliyan 54 na al'ummar Amurka, na dauke da cutar amosanin gabbai, Kuma sanadin cutar, miliyan 24 daga cikin wancan adadi ba sa iya gudanar da ayyukansu na yau da kullum yadda ya kamata.

Wani Rahoton da cibiyar ta fitar a baya-bayan nan, ya bayyana cewa, adadin wadanda cutar ke hana su gudanar da ayyukan nasu yadda ya kamata, ya karu daga kashi 35.9 a shekarar 2002 zuwa kashi 42.8 a shekarar 2014.

Rahoton ya kuma bayyana cewa, kusan kashi 60 cikin dari wato kimanin mutane miliyan 32 dake dauke da cutar na cikin shekarun aiki.

Har ila yau, cibiyar ta ce kimanin rabin baligai na kasar masu fama da ciwon zuciya da na sukari na kuma fama da cutar ta amosanin gabbai.

Cibiyar CDC ta ce cutar amosanin gabbai mai haifar da ciwo da kumburi da kuma cijewar gabbobi na kara yaduwa a cikin jama'a (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China