Mataimakin babban Sufeton 'yan sanda dake Abuja, babban birnin kasar Salisu Fagge, ya ce matakin wani bangare ne na tabbatar da tsaron lafiyar matafiya dake bin titin.
Ya ce ana sa ran samun karuwar zirga-zirgar ababen hawa akan titin nan da makonni shida masu zuwa, saboda mai da zirga zirgar jiragen sama da aka yi daga filin jirgin saman kasa da kasa na Nnmadi Azikwe dake Abuja zuwa filin jirgin saman Kaduna.
An rufe filin jirgin saman Abuja ne a ranar Laraba da ta gabata saboda wasu muhimman gyare-gyare da za a aiwatar, musammam ma akan titin jirgi.
Ya kara da cewa, an umarci kwamishinonin 'yan sanda na jihohin Kaduna da Niger da kuma na birnin Tarayya Abuja su dauki dukkan matakan da suka dace na kawar da duk wata barazanar tsaro akan titin da sauran wurare. (Fa'iza Mustapha)