in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Buhari ya komo Nigeria
2017-03-10 20:53:50 cri
Ran 10 ga wata da misali karfe takwas saura minti 13 da safe, agogon Najeriya, shugaba Buhari na kasar ya sauka a filin jirgin saman na jihar Kaduna, daga baya kuma ya isa fadarsa ta jirgin sama mai saukar ungulu bayan ya shafe kwanaki 50 yana samun jinya a wani asibitin London na kasar Britaniya. Mataimakin shugaba Yemi Osinbajo da dai sauran jami'an gwamnati sun tarbe shi a fadarsa. Bayan shugaba ya iso Abuja, ya gana da ministocinsa na gwamnati da dai sauran shugabanni, ban da wannan kuma, uwargidansa Aisha Buhari da uwargidan Osinbajo Dolapo Osinbajo da dai sauran matan gwamnoni daban-daban sun tarbe shi a dakin taro na Aisha dake fadar shugaba. Duk da cewar Buhari ya komo Nigeria, saboda yin la'akarin da halin lafiyar jikinsa, shugaban Buhari ya ce, zai ci gaba da hutawa, kuma Osinbajo zai ci gaba da gudanar da aiki na shugabancin kasar. (Wakiliya Amina daga Abuja)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China