in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IATA tana bin kamfanin jiragen saman Airik bashin dala miliyan 78
2017-02-28 09:48:23 cri
Kungiyar kula harkokin jiragen sama ta kasa da kasa (IATA) ta bayyana cewa, yanzu haka tana bin kamfanin jiragen saman Arik na Najeriya bashin tsabar kudi dala miliyan 78.

Kakakin kamfanin jiragen saman na Airk Simon Tumba ya shaidawa manema labarai a birnin Legas cibiyar kasuwancin Najeriya cewa, bashin da kungiyar ta IATA ta ke bin kamfanin ya kunshi kudin duba lafiyar jiragen saman kamfanin kamar yadda ya ke kunshe cikin yarjajeniyar da sassan biyu suka kulla.

A kwanakin baya ne dai kungiyar ta dakatar da kamfanin jiragen saman na Arik daga samun hidimominsa saboda tarin basussukan da suka yi kamfanin katutu.

A ranar 9 ga watan Fabrairu ne gwamnatin Najeriya ta sanar da karbar harkokin kamfanin saboda matsalolin kudin da ya ke fuskanta.

Ministan kula da harkokin sufurin jiragen sama na Najeriya Hadi Sirika, ya ce matakin da gwamnati ta dauka kan kamfanin ya zo a lokacin da ya dace, yana mai ba da tabbacin kamfanin zai dawo hayyacinsa.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China