Firaministan kasar Sin Li Keqiang da sauran jagororin kasar sun gana da mambobin majalissar wakilan jama'ar kasar Sin na lardunan daban daban, inda suka tattauna game da batutuwan da suka jibanci tattalin arziki, da bunkasa shirin ziri daya da hanya daya.
Yayin taron na jiya Alhamis, firaministan Li Keqiang, ya zanta da wakilan lardin Shaanxi, inda ya yi kira gare su, da mai da hankali ga bunkasa masana'antu da za su rika sarrafa hajojin fasahar zamani, da na sadarwa, da wadanda za su tallafawa cinikayya ta yanar gizo a yankunan karkara.
Kaza lika ya ja hankulun su game da bukatar kara azama, wajen bunkasa fannin yawon bude ido, da raya al'adu, domin samar da karin guraben ayyukan yi ga al'umma.
A nasa bangare, shugaban zaunannen kwamitin NPC Zhang Dejiang, wanda ya gana da wakilan lardin Jiangsu, cewa ya yi yana da muhimmanci wakilan al'umma daga matakai daban daban, su dage wajen aiwatar da manufofin jam'iyyar kwaminis mai mulkin kasar Sin. Su kuma tabbatar da gudanar ayyukan hukuma bisa tsarin jam'iyya.
Sauran jagororin da suka gana da 'yan majalisar wakilan al'ummar kasar ta Sin sun hada da Yu Zhengsheng, da Wang Qishan, da Zhang Gaoli.(Saminu)