A yau ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi wani muhimmin jawabi mai taken "gina kyakkyawar makoma ta hadin gwiwar kasashen Sin da Koriya ta Kudu, ba da babbar gudumawa wajen neman bunkasuwar yankin Asiya baki daya" a jami'ar Seoul ta kasar Koriya ta Kudu. Cikin jawabinsa, shugaba Xi ya ambaci dangantakar abokantaka dake tsakanin kasashen Sin da Koriya ta Kudu, makomar kasar Sin da kuma hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, inda ya kuma jaddada aniyar kasar Sin wajen tsayawa tsayin daka kan kiyaye zaman lafiyar kasa da kasa da kuma shiyya-shiyya, ciyar da hadin gwiwar kasa da kasa gaba, kuma tana son gina dangantakar abokantaka tare da kasar Koriya ta Kudu don neman ci gaban kasashen biyu, kiyaye zaman lafiya da neman bunkasuwar yankin Aisya cikin hadin gwiwa, har ma da ba da babbar gudummawa kan bunkasuwar kasa da kasa. Bugu da kari, Xi Jinping ya nuna kyakkyawan fatansa ga matasan kasashen biyu don su ci gaba da dangantakar abokantaka dake tsakanin kasashen biyu, da kuma shiga cikin aikin bunkasa yankin Asiya cikin himma da kwazo. (Maryam)