in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta yi maraba da sakin wasu dakarun ta da SPLM ke tsare da su
2017-03-06 10:28:59 cri
Mahukuntan kasar Sudan, sun yi maraba da sakin dakarun sojin kasar su 107, da wasu fararen hula su 18, wadanda a baya ke tsare a hannun mayakan kungiyar 'yan tawayen SPLM tsagin arewaci.

Kungiyar 'yan tawayen SPLM dai ta saki mutanen ne a ranar Lahadi, tuni kuma suka isa birnin Khartoum fadar mulkin Sudan, inda suka hadu da iyalan su.

Da yake jinjinawa wannan mataki na kungiyar SPLM, ministan watsa labarai a Sudan Ahmed Bilal Osman, ya ce gwamnatin kasar ta yi matukar maraba da wannan mataki.

Shi ma wakilin kungiyar bada agajin jin kai ta Red Cross a Sudan Rene Gerard, ya bayyana farin cikin sa game da wannan nasara da aka samu.

Tun cikin shekarar 2011 ne dai kungiyar SPLM ta fara fito na fito da gwamnatin Sudan a jahohin Blue Nile da kudancin Kordofan.

Ya zuwa yanzu an gudanar da zagaye 10 na tattaunawar wanzar da zaman lafiya, tsakanin gwamnatin Sudan da wakilan kungiyar ta SPLM tsagin arewaci a birnin Addis Ababan kasar Habasha, sai dai ba a kai ga cimma nasarar kawo karshen tashe tashen hankula a yankunan 2 ba. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China