in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sudan ta aike da sammaci ga jakadan Amurka a kasar
2017-03-10 09:50:49 cri
Ma'aikatar harkokin wajen Sudan, ta aike da sammaci ga jakadan Amurka dake Khartoum, domin nuna adawa da haramcin shiga Amurka da aka sanyawa 'yan asalin kasar.

Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Sudan din ta fitar, ta ruwaito mataimakin sakataren ma'aikatar harkokin wajen na bayyana takaicin kasar ga jakadan Amurka Steven Koutis game da haramtawa 'yan asalin kasar shiga Amurka.

Sanarwar ta ce Sudan na jiran Amurka ta cire ta daga jerin kasashen dake daukar nauyin ta'addanci, ta na kuma mai kira a gare ta, da su hada hannu wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro da kuma ci gaba.

Sudan din ta kara da cewa, za ta ci gaba da bada hadin kai a kokarin da ake na shawo kan ayyukan ta'addanci tare da cimma tsaro da zaman lafiya a yankin da take da ma duniya baki daya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China