Kamfanin dillanci labarai na SUNA ya ruwaito cewa, matakin da shugaban kasar ya dauka a jiya Laraba na da nufin inganta gwamnatin hadin kai tare da samar da kyakkyawan yanayin cimma zaman lafiya mai dorewa a kasar.
Wasu daga cikin 'yan tawayen sun fito ne daga kungiyoyi masu dauke da makamai dake yaki da gwamnatin kasar a yankin Dafur, yayin da wasu kuma suka fito daga kungiyar 'yan tawaye dake fafutukar samar da yanci ga al'ummar kasar wato SPLM
A ranar Asabar ne kungiyar SPLM bangaren arewa ta saki dakarun gwamnati kusan 107 da ta rike su a matsayin fursunoni.
Tun a shekarar 2011 kungiyar SPLM ta arewa ke yaki da Gwamnatin kasar a yankunan Blue Nile da Kodofan ta kudu. (Fa'iza Mustapha)