Shugaba al-Bashir ya kuma shaidawa taron manema labarai cewa, ana ci gaba da tattaunawa don ganin an cimma matsaya game da mukaman da za a raba a dukkan matakai.
Ya kuma lashi takwabin cewa, jam'iyyar NCP mai mulkin kasar za ta ba da hadin kai don tabbatar da cewa, an kafa gwamnatin da za ta kunshi dukkan bangarorin siyasar kasar.
Sabon firaministan kasar ta Sudan Bakri Hassan Saleh ne zai jagoranci aikin sake fasalta hukumomin gwamnatin kasar.
A jiya Alhamis ne dai sabon firaminsitan na Sudan ya sha rantsuwar kama aiki.(Ibrahim)