Wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce da farko, anyi hasashen samun 'yan gudun hijira 60,000 cikin shekarar 2017, amma cikin watanni biyu na farkon shekarar kawai, an samu adadin da ya zarce 31,000.
Sanarwar ta yi bayanin cewa, kiyasin da aka yi da farko, ya nuna cewa, kashi 80 cikin sabbin zuwan mata da yara ne, ciki har da yara da suka rabu da iyayensu, ta na mai cewa, suna tsananin bukatar taimako, da hukumar ta kula da 'yan gudun hijira da sauran hukumomin kawayenta, ke kokarin samarwa.
Wakiliyar hukumar a kasar Sudan, Noriko Yashida, ta fada cikin wata sanarwa cewa, sun damu matuka da halin da mutanen ke ciki, musammam yara da su ne suka fi wahala. (Fa'iza Mustapha)