in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan mata 'yan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya haura matsakaicin adadin da sauran kasashe ke da su
2017-03-08 12:28:24 cri
Kwanan baya, kawancen majalisun dokokin kasa da kasa ya fitar da wani rahoto mai lakabin 'Mata a majalisun dokoki a shekara ta 2016' a birnin Geneva na kasar Switzerland, inda aka nuna cewa, a bara, adadin yawan mata 'yan majalisun dokokin kasashe daban-daban ya karu da kashi 0.7 bisa dari, idan an kwatanta da na shekara ta 2015, inda adadin ya kai kashi 23.3 bisa dari.

Sai dai duk da haka akwai gibi sosai tsakanin wannan adadi, da burin da kawancen majalisun dokokin kasa da kasa ke bukata, wato yawan mata 'yan majalisun dokoki ya kai kashi 50 bisa dari.

Yayin da ake murnar ranar mata ta duniya yau Laraba, kawancen majalisun dokokin kasa da kasa ya fidda wani sabon rahoto, inda ya tattaro alkaluman da suka shafi yawan matan da suka shiga harkokin majalisun dokoki a kasashe da yankuna sama da 270.

Rahoton dai ya nuna cewa, a halin yanzu a kasar Sin, adadin yawan mata 'yan majalisar wakilan jama'a ya kai kashi 23.7 bisa dari, adadin da ya wuce matsakaicin adadin da sauran kasashen duniya ke da su.

Sakatare-janar na kawancen majalisun dokokin kasa da kasa, Mista Martin Chungong ya ce, karuwar adadin mata 'yan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, ta haifar da babban tasiri ga karuwar matsakaicin adadin mata 'yan majalisun dokoki a fadin duniya.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China