in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Pep Guardiola ya ce zai yi wuya a iya dakatar da Chelsea
2017-03-06 15:05:16 cri
Kocin kungiyar Manchester City Pep Guardiola, ya ce zai yi wuya wata kungiya ta iya dakatar da Chelsea daga jagorancin gasar Firimiya ta bana, kuma muddin Manchester City na fatan samun nasara a gasar, sai ta lashe dukkanin wasannin da za ta buga a nan gaba.

Manchester City dai ta doke Sunderland da 2 da nema, matakin da ya raba tsakanin ta da Chelsea da maki 8. Pep Guardiola dai na takaicin yadda tazara tsakanin kungiyar sa da Chelsea ta yi matukar fadi. Yana mai cewa wannan dai shi ne gaskiyar lamari, "mun yi baya da yawa, kuma mawuyaci ne a iya dakatar da kungiyar Chelsea".(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China