Ita ma kungiyar Leicester City ta samu tagomashi ne a wasanta da Hull City, inda a karo na biyu kasa da mako guda ta samu nasara a gida. Yayin wasan na karshen mako da ya gudana a filin wasa na King Power, Leicester City ta doke Hull City ne da ci 3-1. Hakan dai ya dada raba Leicester City da hadarin fita daga ajin wannan gasa ta Firimiyar Ingila.
Ita kuwa Manchester United canjaras ta yi 1-1 da Bournemouth, a wasan da suka buga a Old Trafford. An dai kai ruwa rana yayin da 'yan wasan na Manchester ke kokarin samun nasara kan abokan karawar ta su, a wasan na karshen mako. Sai dai kuma duk kwazon na su, bai sa kwalliya ta biya kudin sabulu ba.
Yanzu haka dai Chelsea ta na saman teburin na Firimiya da maki 63, sai kuma Tottenham Hotspur a matsayi 2 da maki 56. Yayin da kuma Manchester City ke matsayi na 3 da maki 55.(Saminu Alhassan)