in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kocin Najeriya ya hakura da 'yan wasa dake kwallo a Sin
2017-03-06 15:03:04 cri

Yanzu haka dai wasu banayai sun fara bulla, game da dalilan da suka sanya kocin tawagar kwallon kafar Najeriya Gernot Rohr hakura da 'yan wasan kasar masu taka leda a kasar Sin, musamman yayin wasannin sada zumunta da Super Eagles din za ta buga da kasashen Senegal da Burkina Faso.

'Yan wasan kasar 3 da suka komo Sin ba da dadewa ba, sun hada da John Obi Mikel, da Brown Ideye da kuma Odion Ighalo, a baya na cikin tawagar 'yan wasan da za su buga wadannan wasanni na sada zumunci. Sai dai daga baya Mikel Obi da sauran 'yan wasan biyu sun mika bukatar a zare sunayen su daga wannan jadawali, aka kuma amince masu da hakan.

Dalilin koci Gernot Rohr dai na amincewa da bukatar 'yan wasan shi ne, ganin cewa ya kamata a baiwa 'yan wasan damar sabawa da sabbin kungiyoyin da suke bugawa kwallo a yanzu haka, kafin su fara komawa gida buga wa Super Eagles wasanni.

Sai dai kuma masharhanta na ganin makomar kungiyar na iya fuskantar kalubale, a gabar da koci Rohr ke fafutukar neman 'yan wasan da zai maye gurbin wadannan ukun, daga wasu kulaflikan dake nahiyar turai.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China