A yayin jawabinsa, jakada Song ya bayyana cewa, yanzu haka ana gudanar da manyan taruka biyu na kasar Sin a birnin Beijing, wato taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar, da na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasar kasara. Yayin tarukan biyu na bana, za a dudduba rahotanni guda 6, ciki har da rahoton ayyukan gwamnati, inda 'yan majalisun za su ba da shawarwari kan manyan batutuwan da suka shafi harkokin kasa da na zaman rayuwar jama'a, a sa'i guda za su taka rawa wajen kafa dokoki da sa ido.
Jakada Son ya kara bayyana cewa, ofishin jakadancin kasar Sin dake Masar, na fatan ci gaba da karfafa mu'amala, da hadin kai tare da majalisar dokikin masar, yana kuma mai fatan inganta manufar ziyarar juna a matakai daban daban a tsakanin majalisun dokokin kasashen biyu, da karfafa cudanya tsakanin kwamitocin musamman na majalisun biyu, da nufin ciyar da kyakkyawar dangantakar hadin su gaba.
'Dan majalisar dokokin kasar Masar Nader Mostafa ya bayyana cewa, yin mu'ammala tsakanin majalisun dokoki muhimmiyar hanya ce, ta karfafa dangantakar hadin kai tsakanin kasashen biyu.
A shekarun baya bayan nan, an kara daukar matakan karfafa cudanya, da ziyartar juna a tsakanin sabuwar majalisar dokokin Masar da majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, matakin da zai zurfafa hadin kai da amincewar juna a tsakaninsu. (Bilkisu)