in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hernanes na kasar Brazil yana tuntubar kulob din Fortune na kasar Sin
2017-02-08 17:03:41 cri
Hernanes, dan wasan tsakiya dan asalin kasar Brazil, zai iya zama wani sabon dan wasan nahiyar latin Amurka da zai taka leda a ajin kwararru na kwallon kafar kasar Sin ko CSL.

Wannan dan wasa mai shekaru 31 a duniya, yanzu haka yana tattaunawa tare da kulob din Hebei China Fortune na kasar Sin, bayan da suka raba gari da shugabannin kulob din kasar Italiya Juventus. Hakan ya kasance wani labarin dake yaduwa a kafofin watsa labarun kasar Brazil.

An ce kulob din na kasar Sin ya yarda da baiwa kulob din Juventus kudin da yawansa ya kai Euro miliyan 10, domin samun damar kulla kwangilar shekaru 2 tare da Hernandes.

A kwanakin baya, wasu kuloflikan kasar Sin da suka hada da Shanghai Shenhua, da Shanghai SIPG sun riga sun kulla kwantiragi tare da wasu 'yan wasan kasashen nahiyar latin Amurka, ciki hadda Carlos Tevez da Oscar.

Yanzu haka cikin 'yan wasan kasashen waje da kulob din Hebei China Fortune ke da su akwai dan kasar Argentina Ezequiel Lavezzi, da Gervinho na kasar Kodibwa. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China