A kakar wasa da muke ciki, Costa bai samu wani matsayi mai muhimmanci sosai a Bayern ba, ganin an sanya shi a matsayin daya daga cikin 'yan wasan rukuni na farko na kungiyar ne cikin wasanni 11 kacal, cikin jimillar wasanni 28 da kungiyar ta buga, inda ya zura kwallaye 4 cikin raga.
Sai dai wata kafar watsa labaru ta kasar Brazil ta ba da labarin cewa, dan wasan ya riga ya samu gayyata daga wasu kuloflikan kasar da na wasu na nahiyar Turai. Saboda haka zai zauna ya yi bincike kan lamarin bayan kakar wasa ta bana ta kammala. Duk da haka, Costa ya ce yana son buga kwallo da Bayern Munich, domin samun damar cika burin samun nasara a wasu manyan gasanni,kamar lashe gasar zakarun Turai, da kyautar martaba 'yan wasa ta Golden Ball, da dai sauransu. Amma dan wasan mai shekaru 26 a duniya ya kara da cewa, wasan kwallon kafa tamkar kasuwanci ne, don haka idan wani kulob na daban ya ba da kudi masu yawa, mai yiwuwa ne Bayern Munich ta amince ya sayar da shi.(Bello Wang)