Kulob din Coritiba karkashin tsarin Serie A na kasar Brazil, ya sanar da cewa, ba zai ci gaba da neman Ronaldinho ba, bisa la'akari da yadda dan wasan ya karbi matsayin da kulob din Barcelona ya ba shi, na kasancewa jakadan kulob din. Ya ce irin alakar dake tsakanin Ronaldinho da kulob din Barcelona zai yi tasiri matuka kan ajandar dan wasan a nan gaba.
Dan wasan mai shekaru 36 a duniya ya dade ba ya takawa wani kulob wasa, tun bayan da ya bar kulob din Fluminense dake birnin Rio de Janeiro a watan Satumban shekarar 2015.
Bisa sabon matsayinsa na jakadan Barcelona, ana saran ganin dan wasan, wanda ya taba zama dan wasa mafi kwarewa a duniya har karo 2, yana zagaya sassan duniya, domin halartar bukukuwa daban daban, a wani mataki na bullo da hanyoyin kara daukaka matsayin FC Barcelona a idanun al'ummun duniya. (Bello Wang)