Majalisar, na da alhakin ba shugaban kasa shawarwarin da suka dace yayin da yake gudanar da ayyukansa.
Sannan idan aka tuntube ta ko ma bisa radin kanta, majalisar za ta iya bada shawarwari kan duk wani batu dake gaban shugaban kasa ko wani minista ko kuma wata hukuma da kundin tsarin mulki ya kafa.
Wata sanarwa da daraktan yada labaran fadar shugaban kasar Eugene Arhin ya fitar, ta ce daga cikin mutanen da shugaba Akufo-Addo ya nada, dake jiran sahalewar majalisar dokoki, har da Tsohon babban hafsan tsaro, Janar Joseph Boateng Danquah da Tsohon Sufeto Janar Nana Owusu Nsiah.
Sanarwar ta kara da cewa, la'akari da rashin tsohon babban joji dake raye, shugaban bai mika sunan kowa ga majalisar dokokin domin amincewarta ba. (Fa'iza Mustapha)