in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
FAO: Fari da tashin hankalin sun kara dagula matsalar abinci a Afirka
2017-03-03 10:10:12 cri
Shirin samar da abinci da aikin gona na MDD, FAO a takaice ya yi gargadin cewa, duk da tarin arbarkar noma da aka samu a wasu sassan duniya, a gyefe guda kuma fari da tashe-tashen hankula suna kara ta'azzara matsalar abinci a nahiyar Afirka musamman sassan gabashin nahiyar.

Wani sabon rahoto da shirin na FAO ya fitar wanda ke dubi game da tasiri da halin da ake ciki game da samar da abinci, ya nuna cewa, ana fuskantar matsalar abinci a yankunan da ake fama da tashin hankali.

Bugu da kari, a cewar shirin na FAO yayin da ake fatan samun farfadowar amfanin gona a kasashen da ke kudancin nahiyar Afirka, tashe-tashen hankula na kara haifar da matsalar yunwa tare da raba mutane da muhallansu a wasu sassan duniya.

Yanzu haka dai an ayyana barkewar matsalar yunwa a kasar Sudan ta kudu, inda wasu rahotanni ke cewa kimanin mutane 100,000 a yankunan Leer da Mayendit dake tsohuwar jihar Unity su na fama da matsalar yunwa. Akwai kuma fargabar makamanciyar wannan matsala tana iya barkewa a yankunan makwabta.

A kasar Somaliya kuma, kimanin mutane miliyan 2.9 ne aka yi kiyasin cewa suna fama da matsalar karacin abinci cikin watanni shidan da suka gabata, sakamakon matsalar tsaro da fari, sai kuma mutane miliyan 8. 1 wadanda ke fuskantar wannan matsala ta karancin abinci a yankin arewacin Najeriya.

Wasu kasashen da tashin hankali ya cusa cikin matsalar karin abinci a cewar shirin na FAO, sun hada da Afghanistan, da Burundi, da Jamhuriyar tsakiyar Afirka da jamhuriyar demokiradiyar Congo. Sauran kasashen sun hada da Iraki, da Myammar, da Yemen da kuma Syira. Bayanai na cewa, wannan matsala tana iya shafar miliyoyin mutane har ma da kasashe makwabta da ke karbar 'yan gudun hijira.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China