in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kanayo Nwanze ya lashe lambar yabo ta masu tallafawa samar da abinci a nahiyar Afirka
2016-09-08 10:46:15 cri

Wani kwararre a fannin bunkasa samar da abinci isasshen kuma mai gina jiki 'dan asalin tarayyar Najeriya mai suna Kanayo Nwanze, ya lashe lambar yabo irin ta ta farko a fannin da ya yi fice, daga kwamitin da ke sanya ido kan gudummawa da ake bayarwa a wannan fani.

Nwanze mazaunin birnin Rome na kasar Italiya, wanda ke jagorantar wani asusun kasa da kasa na bunkasa noma ko (IFAD) a takaice, ya karbi wannan lamba ta yabo ne a ranar Laraba, yayin taron kwamitin da tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ke jagoranta a birnin Nairobin kasar Kenya.

Da yake tsokaci yayin mika lambar yabon ga Mr. Nwanze, Obasanjo ya bayyana shi a matsayin mutum na gari, da ya dace ya zama abun misali na irin yadda ya dace jagora ya zamo, wajen sauya akalar na kasa da shi zuwa hanya mai bullewa. Obasanjo ya ce, irin gudummawar da Nwanze ya bayar ba za ta misaltu ba.

Ana ba da wannan lambar yabo ne dai ga mutune, ko cibiyoyi da suka yi fice wajen kawo sauyi ga tsarin da ake bi na samar da isasshen abinci tun daga tushe a yankunan nahiyar Afirka. Kana ana gabatar da tukuicin kudi har dalar Amurka 100,000 ga wanda ya samu wannan lamba ta yabon.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China