in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babu karancin abinci a Tanzaniya, in ji firaministan kasar
2017-01-17 10:43:54 cri

Firaministan kasar Tanzaniya Kassim Majaliwa, ya fada a jiya Litinin cewa, kasar wacce ke gabashin Afrika ba ta fuskanta matsalar karancin abinci, kana ya bukaci al'ummar Tanzaniyan da su guji yada jita jita game da matsalar abinci a kasar.

Majaliwa, ya bayyana hakan ne bayan wasu rahotanni da kafafen yada labaran kasar da wasu shugabannin addinai ke bayyana cewa, kasar Tanzaniyan na fuskantar matsalar karancin abinci.

Charles Tizeba, ministan gona, kiwon dabbobi da kamun kifi na kasar, ya fada a taron manema labarai a babban birnin kasar Dar es Salaam cewa, wasu alkaluma game da samar da abinci a kasar da aka gudanar a watan Yulin shekarar 2016 sun nuna cewa, kasar tana da rarar abinci da ya kai kashi 123 bisa dari.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China