in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sama da mutane miliyan 17 ne ke fuskantar karancin abinci a yankin kahon Afirka
2017-01-30 12:59:03 cri
Hukumar abinci da aikin gona ta MDD FAO, ta ce mutane sama da miliyan 17 ne ke fuskantar karancin abinci a wasu yankuna dake kahon nahiyar Afirka. Wadannan kasashe dai sun hada da Djibouti, da Eritrea, da Habasha, da Kenya. Sauran su ne Somalia, da Sudan ta Kudu, da Sudan da kuma Uganda.

Hukumar ta FAO ta kara da cewa, fari na yaduwa a wannan yanki, tun bayan da aka gamu da karancin ruwan sama tsakanin watannin Oktoba zuwa Disambar bara. Rahotanni dai na cewa kaso daya bisa hudu na ruwan sama aka samu, cikin jimillar wanda aka yi hasashen samu a yankin.

Da take karin haske game da hakan, babbar darakta mai kula da harkokin yanayi da albarkatun kasa ta FAO Maria Helena Semedo, ta yi gargadin cewa, muddin ba a dauki matakan da suka wajaba ba, ko shakka babu akwai yiwuwar fuskantar hadari mai tarin yawa.

Yanzu haka dai akwai mutane da yawansu ya kusa miliyan 12, a kasashen Habasha, da Kenya da Somalia dake bukatar tallafin abinci, yayin da matsalolin karancin kudin shiga, da hatsi, da iri, da madara da nama ke kara ta'azzara. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China