in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawon shakatawa ya ragu a Afirka da kaso 3 bisa dari a shekarar 2015
2016-01-19 10:11:03 cri

Hukuma mai lura da harkokin yawon shakatawa ta MDD wato UNWTO, ta ce, yawan masu zuwa yawon shakatawa nahiyar Afirka daga sauran sassan duniya, ya ragu da kusan kaso 3 bisa dari a shekarar 2015 da ta gabata.

Bisa jimilla mutane miliyan 53 ne suka ziyarci nahiyar a shekarar ta bara, wanda hakan ke nuni da raguwar kaso 8 bisa dari na 'yan yawon shakatawa a arewacin nahiyar, da kuma raguwar kaso 1 bisa dari na yawan masu ziyartar kasashen da ke kudu da hamadar Sahara.

Rahoton binciken da hukumar ta UNWTO ta fitar a birnin Nairobin kasar Kenya, ya kuma nuna cewa, fargabar yanayin tsaro ce ta sanya masu yawon bude ido kauracewa kasashe irin su Kenya, da Najeriya, da Tunisiya da kuma Masar.

Sai dai duk da hakan, rahoton ya bayyana yiwuwar farfadowar harkar yawon shakatawa a kasar Kenya, duba da yadda mahukuntan kasar ke daukar matakan karfafa tsaro a yankunan gabar ruwan kasar.

Da yake tsokaci game da sauran alkaluman da UNWTO ta tattara, sakataren hukumar Taleb Rifai, ya ce, a shekara 2015, yawon shakatawa ya samu bunkasa, matakin da ya ba da damar fafadar tattalin arzikin kasashe da dama, tare da samar da karin guraben ayyukan yi masu yawa.

Mr. Rifai, ya ce, bisa jimilla, an samu karuwar kaso 4.4 bisa dari a wannan fanni a shekarar ta bara, wanda ke wakiltar yawan 'yan yawon bude ido biliyan 1.18 a duniya baki daya.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China