Gwamnatin Kenya ta sanar da kebe dalar Amurka miliyan 100 domin bunkasa bangaren yawon shakatawa, wanda ya karu bisa na kasafin kudin shekarar da ta gabata dake dalar Amurka miliyan 50.
Sakatariyar ma'aikatar kasuwanci da yawon bude ido, madam Phyllis Kandie, ta bayyana a ranar Litinin a yayin wani taron manema labarai a birnin Nairobi cewa, za a yi amfani da kudaden musammun ma wajen tallata kasar Kenya a matsayin wani wurin zuwa yawon shakatawa mai nagarta da tsaro. Haka kuma sauran kudaden, za a kashe su wajen tallata kasar Kenya a ketare a cikin muhimman kasuwanni a bangaren yawon shakatawa, in ji madam Kandie. (Maman Ada)