in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta gabatar da shirin hadin gwiwa tsakanin kasashe daban daban a fannin yanar gizo ko Internet
2017-03-01 19:41:20 cri
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, da ofishi mai kula da bayanan da ake watsawa ta hanyar yanar gizo ko Internet na kasar Sin, sun gabatar da shirin hadin gwiwa tsakanin kasashe daban daban a fannin yanar gizo ko Internet a yau Laraba.

Cikin shirin, an gabatar da ra'ayin kasar Sin dangane da hadin gwiwar da ake yi a fannin yanar gizo tsakanin kasashen duniya, wanda ya fi dora muhimmanci kan samun ci gaba cikin zaman lafiya, da hadin kai don tabbatar da moriyar juna.

Bisa wannan shiri ne, kasar Sin za ta gudanar da hadin gwiwa tare da sauran kasashe a bangaren yanar gizo. Hakan ya kasance karo na farko da kasar Sin ta gabatar da irin wannan shiri, da zummar daidaita harkoki masu alaka da yanar gizo.

Sa'an nan, an tanadi burin da kasar Sin ke neman cimmawa, yayin da take hadin kai tare da sauran kasashe kan harkar yanar gizo, wanda ya kunshi kare mulkin kai, da tsaro, da moriyar kasar, da tabbatar da yaduwar bayanai cikin tsari da oda, da kara hada sassan duniya a waje guda, da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali, da bin dokoki, da zurfafa musayar ra'ayi tsakanin al'adu daban daban, tare da kokarin ganin ci gaban fasahar yanar gizo, ta amfani daukacin al'ummar kasa da kasa.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China