in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin kasar Sin ta tallafawa dalibai 'yan asalin kasar sama da miliyan 90 a bara
2017-03-01 09:43:31 cri
Sama da dalibai Sinawa miliyan casa'in ne suka amfana da tallafin kudi daga gwamnatin kasar Sin a cikin shekarar 2016.

Wani rahoto da ma'aikatar ilimi ta kasar ta fitar, ya bayyana cewa, kasar Sin ta kashe sama da yuan biliyan 168 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 24.4 a bara, adadin da ya haura na 2015 da yuan biliyan 12.85, wajen taimakawa dalibai daga matakin farko har zuwa jami'a.

Rahoton ya ce a tsarin gwamnatin na tilasta yin karatu, daliban sun amfana da kudin makaranta kyauta, ya na mai cewa, an ware wasu yuan biliyan 16.74 don samar da littattafan karatu kyauta ga dalibai miliyan 128.

Daraktan cibiyar tallafawa dalibai ta kasar Tian Zuyin, ya ce kasar Sin za ta inganta kudin da take kashewa dalibai a bana, ta yadda ba za a samu yara suna barin makaranta dalilin matsalar kudi da iyayensu ke fuskanta ba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China