in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: Za a karfafa shirin kula da masu bukatu na musamman
2017-02-27 19:25:15 cri
Mahukuntan kasar Sin sun bayyana aniyar su ta daukar karin matakai, na kiyaye aukuwar hadurra dake haddasa nakasa, tare da samar da karin hidima ga sassan al'ummar kasar masu bukatu na musamman. Za dai a fara aiwatar da wata doka ta inganta wannan fanni, tun daga ranar 1 ga watan Yulin wannan shekara.

Dokar wanda hukumar zartaswar kasar ta Sin ta fitar dauke da sa hannun firaminista Li Keqiang, na kunshe da tanaje tanaje na fadada kulawa da Sinawa masu bukatu na musamman, su kimanin miliyan 85 dake sassan kasar daban daban.

Karkashin tsarin dai an fayyace nauyin dake kan dukkanin sassan hukumomi, game da kula da masu bukatu na musamman, da alkawarin samar da kudade da kayan aiki, ga hukumomi ko cibiyoyin dake bada hidima a wannan fanni. Kaza kila shirin ya kunshi bada tallafin kula da lafiya, musamman ga yara masu nakasa 'yan kasa da shekaru 6, da sauran masu bukatu na musamman dake cikin kangin talauci.

Dokar ta kuma bayyana muhimmancin kara azama, wajen tattara bayanai game da masu bukatu na musamman. A daya hannun kuma, ta bukaci hade sassan kandagarkin kamuwa da cututtuka, da bada jiyya, da kula da lafiyar masu juna biyu da jariran wannan rukuni na al'umma. Sai kuma batun kula da bukatun su na sufuri, da kuma kariya a wuraren ayyuka.

Har ila yau dokar ta tanaji kara kaimi, wajen kare aukuwar hadurra dake haddasa nakasa, a wuraren da ake gudanar da ayyuka masu hadari, kamar masana'antu da wasu hukumomin kasar. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China