in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta karfafa matakan lura da gurbatar iska
2017-02-20 10:04:31 cri

Ma'aikatar kula da muhalli ta kasar Sin, ta ce sashen ta mai lura da nagartar iska da ake shaka, zai fidda wani mizani na awon nagartar iska, ta yadda za a iya gane tasirin matakai da biranen kasar ke dauka, game da yaki da gurbatar iska.

Wata takardar umarni da ma'aikatar ta fitar ta nuna cewa, za a kafa tsarin fitar da alkaluma na watanni shida da na shekara, wadanda za su rika bayyanawa jama'ar kasar halin da ake ciki game da nagartar iska, da kuma jadawalin birane da suka fi ingancin iska, da wadanda suke kurar baya a fannin.

Yanzu haka dai sashen dake kula da nagartar iska na kasar na fitar da alkaluma a duk wata, wanda a cewar ma'aikatar, hakan ba zai wadatar ba, musamman idan ana bukatar samun bayanai na sauyin da ake samu a tsawon lokaci, duba da cewa birane daban daban, na da mabanbantan tsare tsare na masana'antu da makakashi.

Da yake karin haske game da hakan, mataimakin shugaba a sashen sanya ido na ma'aikatar Wu Jiyou, ya ce kamata ya yi a rika tsara jadawalin nagartar iska a biranen kasar Sin, bisa kwazon da ko wane birni ke yi wajen daukar matakai, na rade gurbatar muhalli da gwamnatin kasar ta ba da umarnin aiwatarwa.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China