in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta tura ma'aikata a fannin fasahohi zuwa kauyuka domin yaki da fatara
2017-02-20 09:39:17 cri

Bisa wani shiri da ma'aikatar kimiyya da fasaha, da hadin gwiwar ofishin yaki da fatara da samar da ci gaba na kwamitin zartaswar kasar Sin suka tsara, za a fara tura tawagar ma'aikata a fannin kimiyya da fasaha mai kunshe da mutane 18,000 a ko wace shekara zuwa kauyuka, domin tallafawa da dabarun kauda fatara.

Yankunan da za su ci gajiya daga shirin dai sun kunshi sassan yammacin kasar, wadanda ke da kananan kabilu da tarin jama'a dake fama da matsaloli na talauci.

Kaza lika shirin zai ba da dama ta horas da mutane dake zaune a irin wadannan sassa har 2300 a duk shekara kan dabarun inganta rayuwar su, da yadda za su samawa kan su karin kudaden shiga.

Har wa yau za a kafa wasu cibiyoyin fasahohi 100 a irin wadannan yankuna, da nufin ba da horo na musamman a fannin bunkasa noma. A daya hannun kuma, cibiyoyin bincike da na ilimi dake a gabashin kasar wanda ya ci gaba, za su yi hadin gwiwa da yankunan yammacin kasar wajen inganta dabarun yaki da talauci.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China