Mr. Erik ya ce, umurnin da gwamnatin kasar Sin ta zartas, na haramta cinikin hauren giwa, ya sanya sabon kuzari ga aikin kare giwaye, gami da sauran wasu namun daji dake daf da bacewa daga fadin duniya. Haka kuma ya ce wannan na da babbar ma'ana ga aikin kare namun daji a duniya. (Murtala Zhang)