Sama da shekaru talatin ke nan, da Kasar Morocco ta fice daga kungiyar AU wadda a lokacin ake kira da OAU, sai dai a baya-bayan nan, kasar ta sauya matsayarta, inda ta sanya komawa cikin kungiyar cikin muhimman manufofinta.
Yayin bikin rufe taron da ya gudana a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, Sarkin Morocco Muhammad na VI ya bayyanawa shugabannin na Afrika farin cikinsa na kasancewarsu tare, yana mai cewa ya yi kewarsu.
A cewarsa, duk da Morocco ta fice daga Kungiyar AU, cikin wadancan shekaru, ta kulla alaka mai karfi da galibin kasashen Afrika.
Sarki Muhammad na VI, ya kuma yi alkawarin aiki tare da sauran kasashe mambobin kungiyar, da nufin tabbatar da al'ummar Afrika sun ci moriyar arzikin dake nahiyarsu. ( Fa'iza Mustapha)