in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rantsar da shugabannin AU a taron kungiyar na 28
2017-02-01 12:04:42 cri

A jiya Talata ne aka rantsar da sabbin shugabannin kungiyar hadin kan Afirka ta AU. Cikin wadanda suka sha rantsuwar dai hadda sabon shugaban hukumar zartaswar kungiyar da mataimakin sa.

Kaza lika an rantsar da jami'ai da za su kula da harkokin wanzar da zaman lafiya, da tsaro, da sashen siyasa. Sai kuma na hada hadar cinikayya, da jin dadin jama'a. Kana akwai jami'an lura da samar da ababen more rayuwar jama'a, da makamashi, da raya karkara, da fannin tattalin arziki da kuma bunkasa noma.

Taron AU na 28 da ya kammala a jiya Talata, ya kuma zabi shugaban kasar Guinea Alpha Conde, a matsayin shugaban kungiyar na karba karba.

Da take jawabin ban kwana da mahalarta taron, tsohuwar shugabar hukumar zartaswar AU uwargida Nkosazana Dlamini-Zuma, ta bayyana taron a matsayin wanda ya cimma nasarori da dama, wadanda za su amfani al'ummun nahiyar Afirka baki daya.

A nasa bangaren, sabon shugaban kungiyar Moussa Faki Mahamat, ya ce a shirye yake ya hada kai da sauran masu ruwa da tsaki, wajen aiki tukuru domin cimma nasarar kudurorin da kungiyar ta sanya gaba. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China