Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana a jiya Talata cewa, ya tsawaita lokacin dawowansa gida Najeriya daga London na kasar Burtaniya ne, bayan da sakamakon binciken lafiyarsa da likitoci suka gudanar, ya nuna cewa, shugaban yana bukatar karin lokaci domin ya huta.
Shugaba Buhari wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, ya kuma bukaci al'ummar Najeriya da su kwantar da hankulansu, ya kuma gode musu saboda so da kaunar da suke nuna masa.(The Guardian)
Gwamnatin Najeriya ta dakatar da shirinta na karbo duk wani rance daga asusun ba da lamuni a duniya IMF, tana mai cewa, ka'idojin da asusun ya gindaya sun yi tsauri matuka.(Vangurad)