in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Filin saukar jiragen sama na Hongkong ya karbi karin fasinjoji
2017-02-20 13:37:04 cri
Hukumar kula da filayen saukar jiragen sama ta yankin musamman na Hongkong na kasar Sin ta ba da labari a jiya Lahadi cewa, cikin watan Janairun da ya gabata, babban filin saukar jiragen saman yankin Hongkong ya karbar karin fasinjoji da jiragen sama.

Alkaluman saukar jiragen sama, na nuna cewa, yawan fasinjoji a filin saukar jiragen saman yankin Hongkong, a watan Janariun da ya gabata kadai, ya kai miliyan 6 da dubu 200, jimillar da ta karu da kashi 4.8% idan an kwatanta da na bara. Sa'an nan yawan tashi da saukar jiragen sama daga filin saukar jirgin saman, ya kai 35315 cikin watan Janairun, adadin da ya karu da kashi 0.3% bisa na bara. Haka zalika, yawan kayayyakin da aka kwashe ya kai ton dubu 372, jimillar da ta karu da kashi 3.1% bisa makamancin lokacin na bara.

Rahotanni na cewa, dalilin da ya sa aka samu wannan karuwa, ita ce yadda jama'ar yankin Hongkong suka kai ziyara zuwa sauran kasashe da yankuna yayin bikin sabuwar shekarar bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, kuma karuwar mutanen da suka yi bulaguro zuwa waje ta kai kashi 24%, hakan ya sa ake samun karuwar fasinjojin a filin saukar jiragen saman yankin.

Ban da haka kuma, an ce karuwar an fi samun ta ne a jiragen saman dake zuwa kasar Japan, da nahiyar Turai, gami da kudu maso gabashin Asiya.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China