Shugaban kasar Djibouti Ismail Omar Guelleh ya aza layin dogo na karshe mai aiki da wutar lamtarki a ranar Alhamis da zai hada birnin Djiboutie da Addis-Abeba, babban birnin kasar Habasha.
Bayan fiye da shekara daya da rabi ana aikin, wannan biki na shaida kammala mataki na karshe kafin bikin bude wannan layin dogo mai tsawon kilimoita 752 da kasar Sin ta zuba kudi kuma ta gina.
Sabon layin dogo da al'ummomin kasashen biyu ke jira sosai zai kasance layin dogo mafi sauri a cikin tarihin jiragen kasa a kusurwar Afrika. Tare da saurin gudu na kilomita 120 a duk awa guda, zai taimaka ka'in wajen rage da kwanaki biyu idan aka kwatanta da daukar hanyar mota. Hanyar jirgin kasan dai za ta fara aiki a cikin watan Oktoba mai zuwa.
Haka kuma za'a fara gina wata hanyar jirgin kasa da za ta hada Tadjourah, da ke arewacin Djibouti, da birnin Mekele na kasar Habasa da Sin ta zuba kudi da ginawa.
A cewar wasu alkaluma, kasar Habasha dai na shigo da kayayyaki kusan kashi 90 cikin 100, kasa ce da ke nesa da teku, dukkan kayayyakin suna biyo wa ta Djiboutie da ta zama wata muhimmiyar tashar ruwa ga 'yan kasar Habasha kusan miliyan 95.
Kasashen biyu suna fatan zama wani misali na dunkulewar tattalin arziki a shiyyar da tuni suka hada kansu tun a shekarar 2011 ta hanyar layin wutar lantarki. Haka kuma wasu ayyukan gina bututumin mai da gas na kan hanya tsakanin kasashen biyu. (Maman Ada)