Kamfanin kasar Sin dake aikin shimfida layin dogo na zamani a kasar Kenya ya ce, zai fara shimfida layin na Mombasa zuwa Nairobi a watan Nuwamba.
Mataimakin babban manajan kamfanin na CRBR mai suna Robert Ye ya shaida wa manema labarai a Mombasa cewa, yanzu haka an fara aiki a kan mataki na farko tun kafin lokacin da aka tsara.
Mr Ye yana magana ne a Mombasa bayan da ya karbi karin injunan tarago shida da suka iso kasar. Ya ce, an shaida isowar karin injuna na hada layin dogon. Ana sa ran kammala shimfida layin nan da tsakiyar shekara mai zuwa bayan an kafa tashoshin fiye da 33.
Wasu majiyoyi sun ce, kwangilar samar da kayayyakin da aka rattaba wa hannu a farkon wannan shekarar nan sun hada da injuna jiragen kasa 13 masu kimanin saurin kilomita 100 a cikin awa daya, kuma wadannan taragun za su yi jigila ne a tsakanin layin da ya hada Mombasa da babban birnin na Nairobi.
Bankin kasar Sin na Exim zai ba da kudi kashi 90% a kashin farko na aikin wanda zai kunshi kilomita 472 daga Mombasa zuwa Nairobi. Gwamnatin kasar Kenya kuma za ta samar da sauran kudin.
Babban layin dogon zai hada birnin Mombasa zuwa Uganda, Burundi da Sudan ta Kudu.(Fatimah)