Sergei Lavrov ya yi furucin ne yayin da yake halartar taro kan tsaro na 53, da ya gudana a birnin Munich na kasar Jamus.
A cewarsa, kasar Rasha ba ta son riciki da sauran kasashe, amma za ta yi kokarin kare manufofinta.
Baya ga haka, ya soki kungiyar tsaro ta NATO, inda ya bayyana ta a matsayin wadda ake amfani da ita wajen cacar baki, ya na mai cewa, yadda aka karfafa tsarin kungiyar, zai iya haddasa rikici a duniya.
Ministan harkokin wajen na Rasha ya ce, la'akari da yadda ake jawabai wajen taron, za a iya gano cewa har zuwa yanzu, ba a samu damar kawo karshen yakin cacar baki a duniya ba.
A cewarsa, wasu kasashe sun kafa wani dandali na kasashe masu sukuni domin jagorantar sauran kasashen duniya, inda ya ce a ganinsa, yin hakan ba zai taka rawar gani ba.
Sannan, ya yi kira da a kafa wani sabon tsari a duniya, inda za a tantance matsayin kowace kasa bisa yanayin da take ciki a halin yanzu.
Da aka yi masa tambaya kan ko kasar Rasha ta tsoma baki cikin babban zaben kasar Amurka, Ministan ya ce ya kamata masu yada jita-jita su samar da shaidu don tabbatar da gaskiyar lamarin.(Bello Wang)