A wata sanarwar da baitulmali na Amurkar ya fitar, ya umarci cigaba da yin mu'amala da sashen tsaro na gwamnatin Rasha (FSB) kana ya bukaci cigaba da mu'amalar shigar da kayayyaki, da rarraba su, da musayar fasahar sadarwa tsakanin Amurkar da Rasha.
A watan Disambar bara ne, Obama ya sanya takunkumi ga manyan hukumomin leken asiri guda biyu na kasar Rasha, wato GRU da FSB, da wasu manyan jami'an hukumar leken asiri na GRU su hudu da wasu kamfanoni uku na kasar, bisa zarginsu da taka rawa a harkokin zaben shugaban kasar ta Amurka a bara.
Shugaban Amurka Donald Trump, ya jaddada aniyarsa ta janye takunkumi kan kasar Rasha, muddin Rashar ta amince da taimakawa shirin yaki da ta'addanci da sauran wasu muhimman batutuwa da suka shafi Amurkar.