in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Ghana ya rantsar da sabbin ministoci 12
2017-01-29 12:39:10 cri

Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ya rantsar da sabbin ministoci 12 bayan da majalisar dokokin kasar ta kammala aikin tantance su, inda ya bukace su da su yi aiki tukuru domin biyan muradun 'yan kasar wadanda suka zabi jami'yyar NPP a shekarar da ta gabata.

Da yake jawabi ga sabbin ministocin a daren Juma'ar da ta gabata, Akufo-Addo ya ce rantsar da ministocin babban nauyi ne musamman bisa la'akari da irin amincewar da alummar Ghana suka nuna na neman sauyin gwamnati da salon yadda ake tafiyar da harkokin tattalin arzikin kasar.

Shugaban na Ghana ya bukaci sabbin ministocin da su kare manufofin gwamnati kana su yi taka tsantsan wajen tafiyar da dukiyar kasa. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China