Shugaba Addo ya yi wannan kiran jiya da dare lokacin da ya ke rantsar da ministoci 12 da majalisar dokokin kasar ta tantace don nada su mukaman ministoci.
Ya kuma shaidawa ministocin cewa, al'ummar Ghana sun dora fatansu a kan jam'iyyar NPP wajen farfado da yanayin jin dadin jama'a da tattalin arzikin kasar, wadanda za su kai ga ci gaban kasar ta Ghana.
Bikin rantsar da sabbin ministocin na zuwa kwanaki 11 bayan da aka rantsar da rukuni na 1 mai kunshe da minsitoci 13 a watan da ya gabata. (Ibrahim)