in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sin ya mika sakon alhini ga takwatansa na Pakistan
2016-12-09 10:39:05 cri
Jiya Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika sakon alhini ga takwaransa na kasar Pakistan, sakamakon hadarin wani jirgin sama mai dauke da fasinja na kasar.

Cikin sakon nasa, shugaba Xi ya bayyana cewa, aukuwar wannan hadari ya bakanta masa rai sosai, musamman ma lokacin da ya ji labarin cewa, dukkan fasinjoji da ma'aikatan jirgin sun rasa rayukansu, ciki har da wani dan kasar ta Sin. Shugaba Xi ya mika ta'aziya ga iyalan wadanda suka rasu sakamakon wannan hadarin a madadin gwamnati da al'ummar kasar Sin. Sa'an nan, ya bayyana cewa, mutanen kasar Sin suna goyon bayan al'ummomin kasar Pakistan a ko da yaushe. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China